5 sai kuma Malon da Kiliyon suka rasu, Na'omi kuwa ta rasa mijinta da kuma 'ya'yanta maza biyu.
6 Daga can Mowab, Na'omi ta ji cewa, Ubangiji ya taimaki mutanensa, ya ba su abinci, sai ta tashi daga ƙasar Mowab tare da surukanta.
7 Suka kama hanya zuwa ƙasar Yahudiya.
8 Amma a hanya, sai Na'omi ta ce wa surukanta, “Bari ko waccenku ta koma gidan iyayenta. Ubangiji ya yi muku alheri kamar yadda kuka yi mini alheri, ni da marigayan.
9 Ya sa kuma ko waccenku ta yi aure, ta sami hutawa a gidan miji.” Sa'an nan ta yi bankwana da su ta sumbace su.Sai suka fashe da kuka,
10 suka ce mata, “A'a, mā tafi tare da ke wurin mutanenki.”
11 Amma Na'omi ta ce musu, “Ku koma, 'ya'yana, don me za ku tafi tare da ni? Ina da sauran 'ya'ya maza a cikina ne da za su zama mazajenku?