1 Ga waƙar Sulemanu mafi daɗi.
2 Leɓunanka sun lulluɓe ni da sumba,Ƙaunarka ta fi ruwan inabi zaƙi.
3 Akwai ƙanshi kuma kewaye da kai,Jin amon sunanka yana tunasar da ni.Ba wata matar da za ta ƙi ƙaunarka.
4 Ka ɗauke ni mana, mu gudu,Ka zama sarkina, ka kai ni ɗakinka.Da yake kana nan za mu yi farin ciki,Za mu sha ruwan inabi, mu yi murna da ƙaunarki.Ya dace a ƙaunace ka!