8 Mafi kyau cikin mata, ashe, ba ki san wurin ba?Tafi, ki bi garken,Ki samar wa awakinki wurin kiwoKusa da alfarwan makiyaya.
9 Ke ƙaunatacciyata, kina ɗauke hankalinaKamar yadda goɗiya take ɗauke hankalin ingarmun karusan Fir'auna.
10 Kitsonki yana da kyau a kumatunki,Ya sauka a wuyanki kamar lu'ulu'ai.
11 Mu kuma za mu ƙera miki sarƙar zinariya,A yi miki ado da azurfa.
12 A sa'ad da sarki yake kan kujerarsa,Yana jin daɗin ƙanshin turarena ƙwarai.
13 Ƙaunataccena yana da ƙanshin murLokacin da yake kwance a ƙirjina.
14 Ƙaunataccena kamar furen jeji yakeWanda yake huda a gonar inabi a En-gedi.