1 Ina kwance a gadona dukan dare,Ina mafarki da ƙaunataccena,Na neme shi, amma ban same shi ba.Na kira shi, amma ba amsa.
2 Bari in tashi yanzu in shiga birni,In bi titi-titi, in bi dandali-dandali,In nemi wanda raina yake ƙauna.Na neme shi, amma ban same shi ba.
3 Da matsaran da suke kai da kawowa cikin birni suka gan ni,Sai na tambaye su ko sun ga ƙaunataccena.
4 Rabuwata da matsaran ke nan,Sai na yi kaciɓis da ƙaunataccena.Na riƙe shi, ban sake shi ba,Na kai shi gidanmu, har ɗakin mahaifiyata.
5 Ku 'yan matan Urushalima,Ku rantse da bareyi da batsiyoyi,Ba za ka shiga tsakaninmu ba,Ku bar ta kurum.
6 Wane ne wannan da yake fitowa daga cikin jeji,Kamar tunnuƙewar hayaƙi cike da kayan ƙanshi iri iri na fatake?