1 Kyakkyawa ce ke ƙaunatacciyata.Idonki kamar na kurciya, suna haskakawa daga cikin lulluɓi.Gashinki yana zarya kamar garken awakiDa yake gangarowa daga tuddan Gileyad.
2 Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya,Aka yi mata wanka nan da nan.Ba giɓi, suna nan shar.An jera su tantsai.
3 Leɓunanki ja wur kamar kin shafa jan-baki.Maganarki tana faranta zuciya.Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.
4 Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda yake, kewayayye sumul sumul,Inda aka rataye garkuwoyi dubu na jarumawa.
5 Mamanki kamar bareyi biyu ne,Wato tagwayen barewa, suna kiwo cikin furen bi-rana.