2 Haƙoranki farare fat kamar tunkiyar da aka yi mata sausaya,Aka yi mata wanka nan da nan.Ba giɓi, suna nan shar.An jera su tantsai.
3 Leɓunanki ja wur kamar kin shafa jan-baki.Maganarki tana faranta zuciya.Kumatunki suna haske bayan lulluɓi.
4 Wuyanki kamar hasumiyar Dawuda yake, kewayayye sumul sumul,Inda aka rataye garkuwoyi dubu na jarumawa.
5 Mamanki kamar bareyi biyu ne,Wato tagwayen barewa, suna kiwo cikin furen bi-rana.
6 Har iskar safiya ta huro,Duhu kuma ya kawu,Zan zauna a kan tudun mur,Wato tudun kayan ƙanshi.
7 Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,Ba wanda zai kushe ki!
8 Amaryata, ki taho daga Dutsen Lebanon,Taho daga Lebanon.Ki taho daga ƙwanƙolin Dutsen Amana,Da Dutsen Senir da Harmon,Inda zakuna da damisoshi suke zaune.