1 Na shiga cikin lambuna, budurwata, amaryata,Ina tattara mur da ƙaro.Ina shan zuma da kakinsa.Ina shan ruwan inabi da madara kuma.Ƙaunatattuna, ku ci ku sha, har ku bugu da ƙauna!
2 Ina barci, amma zuciyata na a farke,Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa.Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata,Wadda ba wanda zai kushe ki.Kaina ya jiƙe da raɓa,Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.
3 Na riga na tuɓe tufafina, in sāke sa su kuma?Na wanke ƙafafuna, in sāke ɓata su?
4 Ƙaunataccena ya janye hannunsa daga ƙofa,Zuciyata kuwa tana kansa.
5 Sai na tashi don in buɗe wa ƙaunataccena, ya shigo.Hannuna sharkaf da mur,Yatsuna suna ɗiga da mur sa'ad da na kama hannun ƙofar.