10 Wace ce wannan, kamar ketowar alfijir?Ita kyakkyawa ce mai haske, kamar hasken rana,Ko na wata mai kashe ido.
11 Na gangara zuwa cikin itatuwan almondDomin in ga ƙananan itatuwan da suke a kwarin,Domin in ga ganyayen inabiDa furannin itatuwan rumman.
12 Ina karkaɗuwa, don kin sa in ƙosa saboda ƙauna,Kamar mai korar dawakan karusar yaƙi.
13 Komo, ki komo, ke Bashulamiya,Ki komo, ki komo domin mu ƙara dubanki.Me ya sa kuke so ku dubi Bashulamiya,Sa'ad da take taka rawar zamanin dā?