3 Mamanki kamar bareyi biyu ne, wato tagwayen barewa ne.
4 Wuyanki kamar hasumiyar hauren giwa ne.Idonki kamar tafki ne cikin birnin Heshbon,Kusa da ƙofar Bat-rabbim.Hancinki kyakkyawa ne kamar hasumiyar Lebanon ta tsaron Dimashƙu.
5 Kin ɗaga kanki sama kamar Dutsen Karmel.Kitsattsen gashin kanki kamar shunayya mafi kyau ne,Yakan kama hankalin sarki.
6 Ke kyakkyawa ce ƙaunatacciyata,Kina sa ni jin daɗi a rai.
7 Kina da kyan gani kamar itacen dabino,Mamanki kamar nonnan dabino.
8 Zan hau itacen dabino in tsinko 'ya'yan.Mamanki kamar nonnan inabi suke a gare ni.Numfashinki kamar ƙanshin gawasa ne.
9 Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne.Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena,Ya gangara leɓunan masu barci.