9 Bakinki kamar ruwan inabi mafi kyau ne.Idan haka ne bari ya bulbulo sosai zuwa ga ƙaunataccena,Ya gangara leɓunan masu barci.
10 Ni ta ƙaunataccena ce, yana bukatata.
11 Zo saurayina, bari mu tafi waje,Mu kwana a karkara.
12 Za mu tashi da sassafe, mu duba kurangun inabi,Mu ga ko sun fara tohowa,Ko furanni sun fara buɗewa.Mu ga ko itatuwan rumman sun yi fure.A can zan bayyana maka ƙaunata.
13 Za ka ji ƙanshin shuke-shukeDa na dukan 'ya'yan itatuwa masu daɗi.Na adana maka jin daɗi na dā da na yanzu, ya ƙaunataccena.