1 Da ma a ce kai ɗan'uwana ne, wanda mahaifiyata ta goya,Da in na gamu da kai a titi,Sai in sumbace ka, ba wanda zai kula.
2 Sai in kai ka gidan mahaifiyata,In ba ka gaurayayyen ruwan inabina wanda aka yi da rumman, ka sha.
3 In ta da kai da hannun hagunka,Ka rungume ni da hannun damanka.
4 Ku yi mini alkawari, ku matan Urushalima,Ba za ku shiga tsakaninmu ba.
5 Wace ce take zuwa daga cikin jeji,Kafaɗa da kafaɗa da ƙaunataccenta?A ƙarƙashin itacen gawasa na farkar da ke,A wurin da aka haife ki,Wurin da mahaifiyarki ta haife ki.
6 Kada ki ƙaunaci kowa sai ni,Kada ki rungume kowa sai ni.Ikon ƙauna kamar na mutuwa ne,Ƙarfin kishin ƙauna kamar na mutuwa ne.Yakan kama kamar wuta,Yakan ci kamar gagarumar wuta.