7 Kome yawan ruwa ba zai iya kashe ta ba.Ba rigyawar da za ta nutsar da ita.Duk wanda ya ce zai iya sayen ƙauna da dukiya,Ba abin da zai same shi sai tashin hankali.
8 Muna da 'yar'uwa ƙunƙuma.Me za mu yi idan wani saurayi ya ce yana sonta?
9 Da a ce ita bango ce, da mun gina mata hasumiyar azurfa.Da a ce ita ƙofa ce, da mun yi mata ƙyaure da itacen al'ul.
10 Ni bango ce, doguwa, mamana tantsai tantsai,Na sami kwarjini wurin ƙaunataccena.
11 Sulemanu yana da gonar inabiA Ba'al-hamon, wato wuri mai yawan albarka.Ya yi ijara da waɗansu zaɓaɓɓun manoma.Kowannensu yana biyansa kuɗi, azurfa dubu.
12 Ni ma ina da gonar inabi ta kaina.Kai Sulemanu zan ba ka kuɗi azurfa dubu,Sauran ma'aikata kuma zan ba kowanne ɗari biyu.
13 Aminaina suna kasa kunne ga ƙaunataccena.Ina so in ji muryarka daga cikin lambun.