1 Maganar Ubangiji zuwa ga Yowel, ɗan Fetuwel.
2 Ku dattawa, ku kasa kunne,Bari kowa da kowa da yake cikinYahuza, ya kasa kunne.Wani abu mai kamar wannan ya taɓafaruwa a lokacinku,Ko a lokacin kakanninku?
3 Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa,'Ya'yanku kuma su faɗa wa'ya'yansu,'Ya'yansu kuma su faɗa wa tsaramai zuwa.
4 Abin da ɗango ya bari fara ta ci,Abin da fara ta bari burduduwa taci.
5 Ku farka, ku yi ta kuka, kubugaggu,Ku yi kuka, ku mashayan ruwaninabi,An lalatar da 'ya'yan inabinDa ake yin sabon ruwan inabi da su.
6 Rundunar ta aukar wa ƙasarmu,Tana da ƙarfi, ba ta kumaƙidayuwa,Haƙoranta suna da kaifi kamar nazaki.