6 Sai ku koma wurin Allahnku,Ku yi alheri, ku yi adalci,Ku saurari Allahnku kullayaumin.
7 Ubangiji ya ce, “Ɗan kasuwa wanda yake da ma'aunin algus a hannunsa.Yana jin daɗin yin zalunci.
8 Mutanen Ifraimu sun ce, ‘Hakika, mun zama attajirai,Mun samar wa kanmu dukiya.A cikin harkokinmu ba za a sami wata mugunta ba.’
9 Ni ne Ubangiji Allahnku tun daga ƙasar Masar,Zan kuma sa ku zauna cikin alfarwai,Kamar lokatan ƙayyadaddun idodi.
10 “Na yi magana da annabawa,Ni ne na ba da wahayi da yawa,Da misalai kuma ta wurin annabawa.
11 Idan akwai laifi a Gileyad,Hakika za su zama wofi.A Gilgal ana sadaka da bijimai,Bagadansu za su zama kamar tsibin duwatsuA gyaffan kunyoyin gona.”
12 Kakanmu Yakubu ya gudu zuwa ƙasar Aram,A can Isra'ila ya yi barantaka saboda mace,Saboda mace ya yi kiwon tumaki.