1 Ya mutanen Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allahnku,Gama zunubinku ya sa kun yi tuntuɓe.
2 Ku komo wurin Ubangiji, ku roƙe shi,Ku ce, “Ka gafarta mana zunubanmu,Ka karɓe mu saboda alherinka,Mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.
3 Assuriya ba za ta cece mu ba,Ba kuwa za mu hau dawakai ba.Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu,‘Kai ne Allahnmu,’ ba.A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”
4 Ubangiji ya ce, “Zan warkar musu da riddarsu.Zan kuma ƙaunace su sosai,Gama fushina zai huce.
5 Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila,Isra'ila za ta yi fure kamar lili,Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.
6 Tohonta zai buɗo,Kyanta zai zama kamar itacen zaitun,Ƙashinta kuwa kamar itacen al'ul na Lebanon.
7 Waɗanda za su komo, za su zauna a inuwarta,Za su yi noman hatsi da yawa.Za su yi fure kamar kurangar inabi.Ƙanshinsu zai zama kamar ruwan inabi na Lebanon.
8 Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka?Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma.Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar.Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”
9 Duk wanda yake da hikima, bari ya fahimci abubuwan nan.Duk wanda yake da ganewa, bari ya san abubuwan nan,Gama hanyoyin Ubangiji masu gaskiya ne,Masu adalci kuwa za su yi tafiya a cikinsu,Amma masu zunubi za su yi tuntuɓe a kansu.