6 Sa'ad da suka sami wurin kiwo, suka ƙoshi,Sai suka yi girmankai,Suka manta da ni.
7 Zan zama musu kamar zaki,Kamar damisa zan yi kwanto a gefen hanya.
8 Zan auka musu kamar beyar,Wadda aka ƙwace mata 'ya'ya.Zan yage ƙirjinsu, in cinye su kamar zaki,Kamar mugun naman jeji zan yayyage su.
9 “Zan hallaka ku, ya mutanen Isra'ila!Wane ne zai taimake ku?
10 Yanzu ina sarkinku da zai cece ku?Ina kuma dukan shugabanninku da za su kāre ku?Su waɗanda kuka roƙa, kun ce, ‘Ku naɗa mana sarki da shugabanni.’
11 Da fushina na naɗa muku sarki,Da hasalata kuma na tuɓe shi.
12 “An ƙunshe muguntar Ifraimu,Zunubinsa kuwa an ajiye shi a rumbu.