4 Ba zan yi wa 'ya'yanta jinƙai ba,Domin su 'ya'yan karuwanci ne
5 Gama uwarsu ta yi karuwanci.Ita wadda ta haife su ta yi abin kunya.Gama ta ce, ‘Zan bi samarinaWaɗanda suke ba ni ci da sha,Da ulu, da lilin, da mai, da ruwan inabi.’
6 “Don haka zan shinge hanyarta da ƙaya,Zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita.
7 Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba.Za ta neme su, amma ba za ta same su ba.Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari,Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’
8 “Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai,Da azurfa, da zinariya da yawaWaɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.
9 Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa,Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilinWaɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.
10 Yanzu zan buɗe tsiraicintaA idon samarinta,Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.