15 “Ko da yake mutanen Isra'ila suna karuwanci,Kada kuma mutanen Yahuza su yi laifi.Kada ku tafi Gilgal,Ko ku haura zuwa Bet-awen.Kada ku yi rantsuwa da cewa,‘Har da zatin Ubangiji!’
16 Mutanen Isra'ila masu taurinkai ne kamar alfadari.Ta yaya Ubangiji zai yi kiwonsuKamar 'ya'yan tumaki a makiyaya mai fāɗi?
17 Mutanen Ifraimu sun haɗa kai da gumaka,Sai a rabu da su.
18 Su taron mashaya ne kawai,Karuwai ne kuma.Suna ƙaunar abin kunya.
19 Iska ta ƙunshe su cikin fikafikanta.Za su ji kunyar bagadansu.”