3 Isra'ila ta ƙi abin da yake mai kyau,Don haka abokan gāba sun fafare ta.
4 “Suna naɗa sarakuna, amma ba da iznina ba.Suna naɗa shugabanni amma ba da yardata ba.Suna ƙera gumaka da azurfarsu da zinariyarsu,Wannan kuwa zai zama sanadin halakarsu.
5 Ya mutanen Samariya, ina ƙin maraƙinku na siffa.Ina jin haushinsu ƙwarai!Sai yaushe za su rabu da gumaka?
6 Ai, mai aikin hannu ne ya yi shi a Isra'ila!Gunki ne ba Allah ba ne.Za a farfashe siffar maraƙin Samariya.
7 Gama sun shuka iskaDon haka zu su girbe guguwa.Hatsin da yake tsaye ba shi da zangarniya,Ba zai yi tsaba ba.Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci,
8 Isra'ila kamar kowace al'umma ce.Suna cikin al'ummaiKamar kaskon da ba shi da amfani,
9 Gama sun haura zuwa Assuriya,Kamar jakin jeji da yake yawo shi kaɗai.Mutanen Ifraimu sun yi ijara da abokan tsafinsu.