5 Amma zai ce, ‘Ni ba annabi ba ne, ni manomi ne, gama ƙasa abar mallakata ce tun ina yaro.’
6 Idan wani ya tambaye shi cewa, ‘Waɗannan raunukan da suke a hannuwanka fa?’ Zai ce, ‘Ai, raunuka ne da aka yi mini a gidan abokaina.’ ”
7 “Ka farka, ya kai takobi, ka fāɗa wa makiyayina,Ka fāɗa wa mutumin da yake kusa da ni,Ka sari makiyayin domin tumakin su watse.Zan bugi ƙanana da hannuna,Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
8 Ni Ubangiji na ce sulusi biyu na ƙasar za su hallaka,Sulusi ɗaya ne kawai zai ragu.
9 Sulusi ɗayan da ya ragu kuwa zan tura cikin wuta,Zan tace su da wuta kamar yadda akan tace azurfa,Zan gwada su kamar yadda akan gwada zinariya.Za su kira gare ni,Zan kuwa amsa musu,Zan ce, ‘Su jama'ata ne,’Su kuma za su ce, ‘Ubangiji shi ne Allahnmu.’ ”