1 Mala'ikan da yake Magana da ni ya komo ya farkar da ni kamar yadda akan farkar da mutum daga barci.
2 Sa'an nan ya ce mini, “Me ka gani?”Sai na ce, “Na ga alkuki wanda aka yi da zinariya tsantsa, da kwano a kansa, da fitilu bakwai a kansa, da butoci bakwai a kan kowace fitilar da yake bisa alkukin.
3 Akwai itatuwan zaitun biyu kusa da alkukin, ɗaya a wajen dama da kwano, ɗaya kuma a wajen hagun.”
4 Sai ni kuma na ce wa mala'ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”
5 Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya ce, “Ba ka san abubuwan nan ba?”Na ce, “A'a, ubangijina.”
6 Sa'an nan ya ce, “Wannan ita ce maganar Ubangiji zuwa ga Zarubabel cewa, ‘Ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da Ruhuna,’ in ji Ubangiji Mai Runduna.