1 Na kuma ɗaga idona, sai na ga karusa huɗu suna fitowa daga tsakanin duwatsu biyu. Duwatsun kuwa na tagulla ne.
2 Dawakai aharasai ne suke jan karusa ta fari, ta biyu kuwa akawalai ne suke janta.
3 Na uku kuma dawakai kiliyai ne suke janta, ta huɗu kuwa hurdu ne yake janta.
4 Sa'an nan na ce wa mala'ikan da yake magana da ni, “Mene ne waɗannan, ya ubangijina?”
5 Ya ce mini, “Waɗannan su ne ruhohi huɗu waɗanda suka fito daga sama bayan da sun nuna kansu a gaban Ubangijin duniya duka.
6 Karusar da akawalai suke ja, za ta tafi ƙasar arewa, wadda kuma dawakai kiliyai suke ja, za ta bi su. Wadda kuwa hurde suke ja, za ta tafi ƙasar kudu.”
7 Sa'ad da ingarmun suka fita, sai suka ƙagauta su zagaya duniya don su bincike ta. Ya ce musu kuwa, “Ku tafi, ku bincike duniya, kuna kai da kawowa.” Har kuwa suka yi.