2 Sai mutanen Betel suka aiki Sharezer da Regem-melek da mutanensu su nemi tagomashi a wurin Ubangiji,
3 su kuma tambayi firistocin Haikalin Ubangiji da annabawa, cewa ko ya kamata su yi baƙin ciki da azumi a watan biyar kamar yadda suka saba yi a shekarun baya?
4 Sa'an nan Ubangiji Mai Runduna ya yi mini magana, ya ce,
5 in faɗa wa dukan mutanen ƙasar da firistoci, in ce, “Sa'ad da kuka yi azumi da baƙin ciki a watan biyar da na bakwai dukan shekarun nan saba'in, saboda ni ne kuka yi azumin?
6 Sa'ad da kuma kuke ci, kuna sha, ba don kanku ne kuke ci, kuke sha ba?”
7 Maganar ke nan da Ubangiji ya faɗa ta bakin annabawan dā, a lokacin akwai mutane da arziki cikin Urushalima da garuruwa kewaye da ita, a lokacin kuma akwai mutane a Negeb da gindin tuddai.
8 Ubangiji kuma ya yi magana da Zakariya, ya ce,