1 Ubangiji ya yi magana gāba da ƙasar Hadrak, da kuma gāba da Dimashƙu. Ubangiji ne yake lura da 'yan adam duk da kabilan Isra'ila.
2 Ubangiji kuma yana gāba da Hamat wadda yake kan iyaka, yana kuma gāba da Taya da Sidon ko da yake suna da hikima ƙwarai.
3 Taya ta gina wa kanta kagara,Ta kuma tara azurfa kamar ƙura,Zinariya kuma kamar sharar titi.
4 Amma Ubangiji zai washe ta,Ya zubar da dukiyarta a cikin teku,Wuta kuma za ta cinye ta.