1 Ku yi koyi da ni kamar yadda nake koyi da Almasihu.
2 Ina yaba muku ne don kuna tunawa da ni a cikin kowace harka, kuna kuma riƙe ka'idodin nan da kyau, daidai yadda na ba ku.
3 Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne.
4 Duk mutumin da ya yi addu'a ko ya yi annabci kansa a rufe, ya wulakanta shugabansa ke nan.