7 Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.
8 (Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba, amma matar daga jikin namiji take.
9 Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.)
10 Shi ya sa ya kamata mace ta rufe kanta, wato, alamar ikon namiji, saboda mala'iku.
11 Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.
12 Wato, kamar yadda mace take daga namiji, haka namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.
13 Ku kanku ku duba fa ku gani. Ya dace da mace ke nan ta yi addu'a ga Allah da kanta a buɗe?