1 Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,
2 domin kun san umarnin nan da muka yi muku da iznin Ubangiji Yesu.
3 Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,
4 kowannenku kuma ya san yadda zai auro matarsa da tsarki da mutunci,
5 ba ta muguwar sha'awa ba, yadda al'ummai suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.
6 A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.