3 Duk wanda yake wata koyarwa dabam, bai kuwa yarda da sahihiyar maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwar da ta dace da bautar Allah ba,
4 girmankai ya ciccika shi ke nan, bai san kome ba, yana da muguwar jarabar gardama da jayayya a kan maganganu kawai, waɗanda suke jawo hassada, da husuma, da yanke, da mugayen zace-zace,
5 da kuma yawan tankiya a cikin mutane masu ɓataccen hankali, waɗanda har gaskiya ta ƙaurace musu, suna tsammani bin Allah hanya ce ta samu.
6 Bin Allah a game da wadar zuci kuwa riba ce mai yawa.
7 Don ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu iya fita da kome ba.
8 To, in muna da abinci da sutura, ai, sai mu dangana da su.
9 Masu ɗokin yin arziki kuwa, sukan zarme da jaraba, su fāɗa a cikin tarko, suna mugayen sha'awace-sha'awace iri iri na wauta da cutarwa, irin waɗanda suke dulmuyar da mutane, su kai ga lalacewa da hallaka.