2 ina roƙonku kada ku tilasta ni in matsa muku sa'ad da na zo, gama na tabbata zan iya tsaya wa waɗanda suka ce abin da muke yi sha'anin duniya ne.
3 Ko da yake a cikin jiki muke tafiya, famarmu ba irin na mutuntaka ba ne.
4 Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi.
5 Muna ka da masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.
6 A shirye muke kuma mu hori kowane marar biyayya, muddin biyayyarku ta tabbata.
7 Ku dubi abin da yake bayyane mana! in dai wani ya amince na Almasihu ne, to, ya ƙara tunawa, wato kamar yadda yake shi na Almasihu ne, mu ma haka muke.
8 Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba zan kunyata ba.