1 Da ma a ce ku jure 'yar wautata. Ku dai yi haƙuri da ni!
2 Ina kishi a kanku saboda Allah. Gama na bashe ku ga Almasihu, domin in miƙa ku kamar amarya tsattsarka ga makaɗaicin mijinta.
3 Amma ina tsoro kada yă zamana, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa'u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Almasihu.
4 Don in wani ya zo yana wa'azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa'azi, ko kuma in kun sami wani ruhu dabam da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara dabam da wadda kuka yi na'am da ita, ashe, har kuna saurin yin na'am da irinsu ke nan!