16 Ina sāke faɗa, kada wani ya zaci ni wawa ne. In kuwa kun zaci haka nake, to, ku ji ni wawa ne, don ni ma in samu in taɓa 'yar taƙama kaɗan.
17 Abin nan da nake faɗa fa, ba bisa ga umarnin Ubangiji nake faɗa ba, sai dai magana ce irin ta wawa, wadda yake yi gabagaɗi, yana fariya,
18 da yake mutane da yawa suna fariya irin ta 'yan adam kawai, ni ma zan yi.
19 Ai, ku kam, hikimarku har ta kai ga jure wa wawaye da murna!
20 Don in wani ya sa ku bauta, kukan jure masa, ko ya yi muku ƙwace, ko ya more ku, ko ya nuna muka isa, ko kuwa ya mare ku.
21 Mu kam, saboda rauninmu, wane mu da yin haka!Amma ta ko yaya wani yake ƙarfin halin yin fariya, ina magana a kan ni wawa ne fa! to, ni ma sai in yi.
22 In su Ibraniyawa ne, ni ma haka. In su Isra'ilawa ne, ni ma haka. In su zuriyar Ibrahim ne, ni ma haka.