1 Wato, har ila yau, yabon kanmu za mu fara yi kuma? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi?
2 Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu ta yabo, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă san ta, ya kuma karanta ta.
3 A fili yake, ku wasiƙa ce ta Almasihu, ta hannunmu, ba kuwa rubutun tawada ba ne, amma na Ruhun Allah Rayayye ne, ba kuwa a kan allunan dutse aka rubuta ta ba, sai dai a zuci.
4 Wannan ita ce irin amincewarmu ga Allah ta wurin Almasihu.
5 Ba domin mun isar wa kanmu ba ne, har da za mu ce mu ne muke gudanar da wani abu, a'a, iyawarmu daga Allah take,
6 domin shi ne ya iyar mana muka zama masu hidima na Sabon Alkawari, ba alkawarin rubutacciyar ka'ida ba, sai dai na Ruhu. Don kuwa rubutacciyar ka'ida, kisa take yi, Ruhu kuwa, rayarwa yake yi.
7 Aka zana hidimar Shari'ar Musa, wadda ƙarshenta mutuwa ce, a allunan duwatsu. An bayyana hidimar nan da babbar ɗaukaka, har Isra'ilawa suka kasa duban fuskar Musa saboda tsananin haskenta (ga ta kuwa mai shuɗewa ce).