1 Da yake kuma muna aiki tare da Allah, muna roƙonku kada ku yi na'am da alherin Allah a banza.
2 Domin ya ce,“Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa,Na kuma taimake ka a ranar ceto.”Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!
3 Ba ma zamar wa kowa sanadin tuntuɓe, don kada a aibata aikinmu,
4 Amma ta kowace hanya muna bayyana gaskiyarmu, a kan bayin Allah muke, ta matuƙar jurewa, da shan wahala, da ƙuntata, da masifu,
5 da shan dūka, da shan ɗauri, da yawan hargitsi, da yawan fama, da rasa barci, da kuma rasa abinci.
6 Muna kuma bayyana gaskiyarmu ta halin tsarkaka, da sani, da haƙuri, da kirki, da Ruhu Mai Tsarki, da sahihiyar ƙauna,