4 Shi ne magabci, mai ɗaukaka kansa, yana gāba da duk abin da ya shafi sunan Allah, ko kuma wanda ake yi wa ibada. Har ma yakan zauna a Haikalin Allah, yana cewa, shi ne Allah.
5 Ashe, ba ku tuna ba, nakan gaya muku haka tun muna tare?
6 To, a yanzu dai kun san abin da yake tare shi, don kada ya bayyana kafin lokacinsa.
7 Ko a yanzu ma tawayen nan, wanda ba shi fahimtuwa, an fara shi, amma farawar abin da zai faru, sai an ɗauke wanda yake hana shi tukuna.
8 A sa'an nan ne fa sarkin tawayen zai bayyana, Ubangiji Yesu kuwa zai hallaka shi da hucin bakinsa, ya kuma shafe shi da bayyanarsa a ranar komowarsa.
9 Mai tawayen nan kuwa, zai zo ne bisa ga ikon Shaiɗan, yana aikata abubuwan al'ajabi, da alamu, da aikin dabo na ƙarya iri iri,
10 yana kuma yaudarar waɗanda suke a hanyar hallaka, muguwar yaudara, domin sun ƙi ƙaunar gaskiya har yadda za su sami ceto.