3 Amma Ubangiji mai alkawari ne, zai kuwa kafa ku, ya tsare ku daga Mugun nan.
4 Mun kuma amince da ku a game da Ubangiji, cewa kuna bin umarnin da muka yi muku, za ku kuma riƙa bi.
5 Ubangiji yă tattaro hankalinku a kan ƙaunar nan ta Allah, da kuma jimirin nan na Almasihu.
6 To, 'yan'uwa, muna yi muku umarni da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu, ku fita daga sha'anin kowane ɗan'uwa malalaci, wanda ba ya bin ka'idodin da kuka samu a wurinmu.
7 Ai, ku kanku kun san yadda ya kamata ku yi koyi da mu, domin sa'ad da muke a tare, ba mu nuna muku lalaci ba,
8 ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nawaita wa kowane ɗayanku.
9 Ba don ba mu da halaliya a wurinku ba ne, a'a, sai dai don mu zama abin misali a gare ku kawai, don ku yi koyi da mu.