1 Daga Bulus, manzon Almasihu Yesu da yardar Allah, don sanar da alkawarin nan na rai wanda yake ga Almasihu Yesu,
2 zuwa ga Timoti ƙaunataccen ɗana.Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uba, da na Almasihu Yesu Ubangijinmu su tabbata a gare ka.
3 Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa'ad da nake tunawa da kai a cikin addu'ata ba fāsawa.
4 Sa'ad da nake tunawa da hawayenka, nakan yi began ganinka dare da rana, domin in yi farin ciki matuƙa.
5 Ina tunawa da sahihiyar bangaskiyarka, wadda da farko take tare da kakarka Loyis, da mahaifiyarka Afiniki, a yanzu kuma na tabbata tana tare da kai.
6 Saboda haka, ina so in faɗakar da kai, ka lura baiwar nan ta Allah, wadda take tare da kai ta wurin ɗora maka hannuwana.
7 Ai, Allah ba halin tsoro ya ba mu ba, hali mai ƙarfi ne, mai ƙauna, da kuma kamunkai.