13 Sai Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafusa a jirgin ruwa, suka isa Bariyata ta ƙasar Bamfiliya. Yahaya kuwa ya bar su, ya koma Urushalima.
14 Amma suka wuce gaba daga Bariyata, suka tafi Antakiya ta ƙasar Bisidiya. Ran Asabar kuma sai suka shiga majami'a suka zauna.
15 Bayan an yi karatun Attaura da littattafan annabawa, shugabannin majami'ar suka aika musu, suka ce, “'Yan'uwa, in kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama'a, ai, sai ku yi.”
16 Sai Bulus ya miƙe, ya ɗaga hannu a yi shiru, ya ce,“Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, da sauran masu tsoron Allah, ku saurara!
17 Allahn jama'ar nan Isra'ila ya zaɓi kakanninmu, ya ɗaukaka jama'ar sa'ad da suke baƙunci a ƙasar Masar, da maɗaukakin iko kuma ya fito da su daga cikinta.
18 Wajen shekara arba'in yake haƙuri da su cikin jeji.
19 Ya kuma hallaka al'umma bakwai a ƙasar Kan'ana, sai ya raba musu ƙasar tasu gādo, suka zauna har shekara arbaminya da hamsin.