1 Sa'ad da muka rabu da su da ƙyar, muka shiga jirgi muka miƙa sosai zuwa tsibirin Kos, kashegari kuma sai Rodusa, daga nan kuma sai Batara.
2 Da muka sami jirgi mai hayewa zuwa ƙasar Finikiya, muka shiga muka tafi.
3 Da muka tsinkayo tsibirin Kubrus, muka mai da shi hagun, muka ci gaba zuwa ƙasar Suriya, muka sauka a Taya, don a nan ne jirgin zai sauke kayansa.
4 Da muka sami inda masu bi suke, muka zauna a nan kwana bakwai. Sai Ruhu ya iza su suka gaya wa Bulus kada ya je Urushalima.
5 Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.
6 Sai muka shiga jirgi, su kuma suka koma gida.
7 Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da 'yan'uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu.