1 To, da Festas ya iso lardinsa, bayan kwana uku sai ya tashi daga Kaisariya ya tafi Urushalima.
2 Sai manyan firistoci da manyan Yahudawa suka kai ƙarar Bulus gunsa, suka roƙe shi
3 ya kyauta musu, ya aika a zo da shi Urushalima, alhali kuwa sun shirya 'yan kwanto su kashe shi a hanya.
4 Amma Festas ya amsa ya ce, “Bulus yana a tsare a Kaisariya, ni ma kuwa da kaina ina niyyar zuwa can kwanan nan.”
5 Ya kuma ce, “Saboda haka, sai waɗansu manya a cikinku su taho tare da ni, in kuwa mutumin nan na da wani laifi, su yi ƙararsa.”
6 Bai fi kwana takwas ko goma a wurinsu ba, sai ya tafi Kaisariya. Kashegari kuma ya zauna a kan gadon shari'a, ya yi umarni a zo da Bulus.