2 Sai manyan firistoci da manyan Yahudawa suka kai ƙarar Bulus gunsa, suka roƙe shi
3 ya kyauta musu, ya aika a zo da shi Urushalima, alhali kuwa sun shirya 'yan kwanto su kashe shi a hanya.
4 Amma Festas ya amsa ya ce, “Bulus yana a tsare a Kaisariya, ni ma kuwa da kaina ina niyyar zuwa can kwanan nan.”
5 Ya kuma ce, “Saboda haka, sai waɗansu manya a cikinku su taho tare da ni, in kuwa mutumin nan na da wani laifi, su yi ƙararsa.”
6 Bai fi kwana takwas ko goma a wurinsu ba, sai ya tafi Kaisariya. Kashegari kuma ya zauna a kan gadon shari'a, ya yi umarni a zo da Bulus.
7 Da ya zo, Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi a tsaitsaye, suna ta kawo ƙararraki masu yawa masu tsanani a game da shi, waɗanda ma suka kasa tabbatarwa.
8 Amma Bulus ya kawo hanzarinsa ya ce, “Ni ban yi wani laifi game da shari'ar Yahudawa, ko Haikali, ko a game da Kaisar ba, ko kaɗan.”