32 ‘Ni ne Allahn kakanninka, Allahn Ibrahim da Ishaku da Yakubu.’ Sai jikin Musa ya ɗauki rawa, bai kuma iya ƙarfin halin dubawa ba.
33 Sai Ubangiji ya ce masa, ‘Tuɓe takalminka, domin wurin da kake tsayen nan, tsattsarka wuri ne.
34 Hakika, na ga wulakancin da ake yi wa mutanena da suke Masar, na ji nishinsu, na kuma sauko don in cece su. To, a yanzu sai ka zo in aike ka Masar.’
35 “To, shi Musan nan da suka ƙi, suna cewa, ‘Wa ya sa ka shugaba kuma alƙali?’ shi ne Allah ya aiko ya zama shugaba, da mai ceto, ta taimakon mala'ikan nan da ya bayyana a gare shi a cikin kurmin nan.
36 Shi ne kuwa ya fito da su, bayan ya yi abubuwan al'ajabi da mu'ujizai a ƙasar Masar, da Bahar Maliya, da kuma a cikin jeji, har shekara arba'in.
37 Wannan shi ne Musan da ya ce wa Isra'ilawa, ‘Allah zai tasar muku da wani annabi daga cikin 'yan'uwanku, kamar yadda ya tashe ni.’
38 Shi ne kuma wanda yake a cikin Ikkilisiyar nan a jeji tare da mala'ikan da ya yi masa magana a Dutsen Sinai, tare da kakanninmu kuma. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana domin ya kawo mana.