1 Daga Bulus, manzo, ba kuwa manzon mutum ba, ba kuma ta wurin wani mutum ba, sai dai ta wurin Yesu Almasihu, da Allah Uba, wanda ya tashe shi daga matattu,
2 da kuma dukan 'yan'uwa da suke tare da ni, zuwa ga ikilisiyoyin ƙasar Galatiya.
3 Alheri da salama na Allah Uba su tabbata a gare ku, da na Ubangijinmu Yesu Almasihu,
4 wanda ya ba da kansa saboda zunubanmu, domin yă cece mu daga mugun zamanin nan, bisa ga nufin Allahnmu, wato Ubanmu.
5 Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin.
6 Na yi mamaki yadda nan da nan kuke ƙaurace wa wanda ya kira ku, bisa ga alherin Almasihu, har kuna koma wa wata baƙuwar bishara,
7 alhali kuwa ba wata bishara dabam, sai dai akwai waɗansu da suke ta da hankalinku, suna son jirkitar da bisharar Almasihu.