26 Domin dukanku 'ya'yan Allah ne, ta wurin bangaskiya ga Almasihu Yesu.
27 Duk ɗaukacinku da aka yi wa baftisma ga bin Almasihu, kun ɗauki halin Almasihu ke nan.
28 Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu.
29 In kuwa ku na Almasihu ne, ashe, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda ne kuma bisa ga alkawarin nan.