3 Ina sāke tabbatar wa duk wanda ya yarda a yi masa kaciya, cewa wajibi ne ya bi dukkan Shari'a.
4 Ku da kuke neman kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, kun katse daga Almasihu ke nan, kun noƙe daga alherin Allah.
5 Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.
6 In muna a cikin Almasihu Yesu, kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba. Bangaskiya mai aikata ƙauna ita ce wani abu.
7 Dā, ai, kuna ci gaba sosai. Wane ne ya hana ku bin gaskiya?
8 Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.
9 Ai, ɗan yisti kaɗan, yake game dukkan curin gurasa.