15 Kaciya da rashin kaciya ba a bakin kome suke ba, sai dai sabuwar halitta ita ce wani abu.
16 Salama da jinƙai su tabbata ga duk masu bin ka'idar nan, wato Isra'ilar gaske ta Allah.
17 Daga nan gaba kada kowa ya ƙara damuna, domin a jikina ina da tabbai masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.
18 Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu yă tabbata a gare ku, 'yan'uwa. Amin.