3 wanda shi ne taska, wato maɓoyar dukkan mafifitan hikima da sani.
4 Na faɗi wannan ne don kada kowa ya hilace ku da maganar yaudara.
5 Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.
6 Da yake kun yi na'am da Almasihu Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya a gare shi,
7 kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.
8 Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.
9 Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata.