1 Tun da yake mutane da yawa sun ɗauka su tsara labarin waɗannan al'amura da suka tabbata a cikinmu,
2 daidai yadda waɗanda suke shaidu tun farkon al'amari, masu hidimar Maganar, suka rattaba mana,
3 da yake kuma na bi diddigin kowane abu daidai tun farko, ni ma dai na ga ya kyautu in rubuta maka su bi da bi, ya mafifici Tiyofalas,
4 domin kă san ingancin maganar da aka sanar da kai baki da baki.
5 A zamanin Hirudus, Sarkin Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na ƙungiyar Abaija. Yana auren wata a cikin zuriyar Haruna, sunanta Alisabatu.
6 Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna bin umarnin Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.