19 Sai mala'ikan ya amsa ya ce, “Ni ne Jibra'ilu da yake tsaye a gaban Allah. An aiko ni ne in yi maka magana, in kuma yi maka wannan albishir.
20 To, ga shi, za ka bebance, ba za ka iya magana ba, sai a ran da al'amuran nan suka auku, don ba ka gaskata maganata ba, za a kuwa cika ta a lokacinta.”
21 Jama'a suna ta jiran Zakariya, suna mamakin jinkirinsa a Haikali.
22 Da ya fito, ya kāsa yi musu magana. Sai suka gane lalle an yi masa wahayi ne a Haikalin. Sai ya riƙa yi musu nuni, amma ba ya magana.
23 Sa'ad da kuma kwanakin hidimarsa suka cika, ya koma gida.
24 Bayan kwanakin nan mata tasa Alisabatu ta yi ciki. Sai ta riƙa ɓuya har wata biyar, tana cewa,
25 “Haka Ubangiji ya yi mini a kwanakin da ya dube ni da rahama, domin yă kawar mini da wulakanci a wurin mutane.”