29 Amma ta damu ƙwarai da maganar, ta yi ta tunani ko wannan wace irin gaisuwa ce.
30 Mala'ikan kuma ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.
31 Ga shi kuma, za ki yi ciki, ki haifi ɗa, ki kuma sa masa suna Yesu.
32 Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki.Ubangiji Allah zai ba shi kursiyin ubansa Dawuda,
33 Zai kuma mallaki zuriyar Yakubu har abada,Mulkinsa kuwa ba shi da matuƙa.”
34 Sai Maryamu ta ce wa mala'ikan, “Ƙaƙa wannan zai yiwu, tun da yake ba a kai ni ɗaki ba?”
35 Mala'ikan ya amsa mata ya ce,“Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki,Ikon Maɗaukaki kuma zai lulluɓe ki.Saboda haka Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.