15 Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.
16 “Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”
17 Sai kuma saba'in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!”
18 Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya.
19 Ga shi, na ba ku ikon taka macizai da kunamai, ku kuma rinjaye a kan dukan ikon Maƙiyi, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan.
20 Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”
21 A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri.